Site icon Popular News

Mun Assasa Kasuwa Ne Da Masallaci Dan Bunƙasa Tattalin Arziki Da Cigaban Addini – Jibrin Kofa

Daga Babangida Sunusi, Kano

A jiya juma’a ne aka buɗe katafariyar kasuwar manoma mai shaguna ɗari biyu da babban masallacin juma’a a garin nasarawan kofa da tsohon ɗan majalisar tarayya da ya wakilci Ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji watau Hon ABDULMUMINI JIBRIN KOFA ya gina dan samama matasa aikin yi da hanyar dogaro da kai a yankin nasa.

Shagunan kasuwar da suka Kai kimani shago ɗari biyu tare da masallaci mai cin kusan mutum dubu biyar a sahu,yayin gudanar da sallah ta juma’a da sauran kamsul salawati da ya bayyana ya ginashi tare da sadaukar dashi ga abokinsa marigayi Umar da Allah yayi ma rasuwa kimanin shekaru 13 kenan.

Sauran wurare da aka buɗe sun haɗa da katafaren gidan mai kai 40 da makewayi na mata da kusan 60 da gurin fakin na manyan motoci da zai ɗauki mota ɗari da wani abu.

Haka zalika acikin jawaban tsohon ɗan majalisar tarayya yace acikin wannan watanne yake sa ran kammala ginin ofishin jami’an tsaro na ‘yan sanda da asibiti dan bunƙasa tsaro da kula da lafiyar al’ummar yanki.

Kofa da ya samu bakuncin shugaban majalisar tarayya na ƙasa da ɗan takarar gwamnan jihar Kano ƙarƙashin jam’iyyar NNPP Engr Abba Kabir Yusuf da ya wakilci shugaban ɗarikar kwankwasiya Dr Rabiu Musa Kwankwaso Kuma ɗan takarar shugaban ƙasar nan a zaɓe mai zuwa, ya tabbatar masu da cewa hakan na nufin samama matasa aikin yi da bunkyasa tattalin arzikin jihar kano dama ƙasa baki tare da bunƙasa harkokin addini.

Hon. Kofa ya kuma ƙara da cewa ita wannan kasuwa ta kayan amfanin gona zata ƙara taimakama manoman jihar kano da ƙasa baki ɗaya,sannan kuma cikinta za’a samama ‘yan kasuwa ɗakunan kwana da masu fakin ɗin manyan motoci yayin da suka yada zangonsu daga ko’ina suke.

Yakuma nanata cewa kasuwa da sauran sassanta ya daukeshi kimanin shekara goma yana aikinta, amma babbar nasarar shine sunfara ɗaukar matasa ɗari biyar aiki wanda kuma yana sa ran ɗaukar kimanin matasa sama da dubu biyu aiki nan gaba idan kasuwar ta kankama.

Daga karshe ya nuna matuƙar godiyarsa ga dukkan waɗanda suka samu halartar wannan taro tun daga kan ma’aikatan gwamnati da manyan ‘yan kasuwa da sauran al’ummma da ‘yan siyasa r ciki da wajen jihar Kano tare da fatan alkhairi garesu.

Exit mobile version