Site icon Popular News

Zaɓen Fidda Gwanin PDP: Dauda Dare Ya Lashe Takarar Gwamna A Zamfara

Daga Hussaini Ibrahim Gusau

Dauda Lawal Dare, ya lashe zaɓen fidda gwamni na takarar kujerar gwamna na jamiyyar PDP a Zamfara, da kuri’a ɗari huɗu da talatin daya. (432)

Jami’in kula da zaɓen Ambasada Adamu Maina Waziri, ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala zaɓen a shalkwatar jamiyyar ta jiha da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Ambasada Waziri ya ƙara da cewa, ‘yan takara huɗu ne suka tsaya takara, wanda suka haɗa da, Eng, Ibrahim Shehu wanda ya samu kuri’a biyar. Sai kuma Wadatau Madawaki ya samu kuri’a uku, sai kuma Hafiz Usman Nahuce bai samu kuri’a ko ɗaya ba, sai kuma Dauda Lawal Dare ya samu kuri’a dari huɗu da talatin da ɗaya. Inji Ambasada Waziri Maina.

Tun kafin lokacin fara kaɗs kuri’a , sai ‘yan takara uku suka fice daga ofishini jamiyyar PDP, suka janye delegates in su da sunan zaba’ayi masu adalci.

‘Yan takara da suka kaurace ma zaɓen sun hada da, Eng. Ibrahim shahe da Hafiz Usman Nahuce da Wadatau Madawaki.

Exit mobile version