Daga Muhammad Maitela
A zaɓen fidda-gwani da jam’iyyar PDP ta gudanar na gwamnoni a jihohin Yobe da Borno, sakamakon ya tabbatar da Hon. Sheriff Abdu Gashuwa a matsayin wanda ya lallasa abokan takarar sa a zaɓen share-fagen da ya gudana a ranar Laraba, a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Hon. Shariff Abdu ya samu nasarar ne biyo bayan samun kuri’u 295 fiye da sauran abokan takarar.
Sai Dr Ali Adamu Tikau, daga kudancin Yobe wanda ya samu kuri’u 129 yayin da shi kuma Abba Gana Tata daga gabashin Yobe ya samu yawan kuri’u 109.
Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Baturen zaɓen mai sanya ido kan gudanar da zaɓen PDP a jihar, Dr Aminu Taura Abdullahi ya ce kimanin kuri’u 539 ne aka jefa a zaɓen, wanda kuri’u kaɗan ne suka lalace.
A hannu guda, a can jihar Borno kuma, Mohammed Jajari ne ya samu nasarar lashe zaɓen fidda-gwani jam’iyyar PDP a jihar.
Sakamakon ya bayyana cewa Jajari ya samu yawan kuri’u 487 wanda ya doke abokin hammayarsa Mohammed Imam mai kuri’u 362 a zaɓen na ranar Laraba.
A sa’ilin da yake sanar da sakamakon zaɓen, shugaban kwamitin zaɓen, Abdulrahman Bobboi, shi ne ya ayyana Mohammed Jajari a matsayin wanda ya samu nasarar da kuri’u 487.
Har wala yau, Bobboi ya ƙara da cewa yawan kuri’un da aka jefa a zaɓen kimanin 849.
Haka zalika kuma, ya buƙaci sauran ‘yan takarar da su ka faɗi da cewa su amince da sakamakon zaɓen da zuciya xaya tare da fawwala wa Allah ga wanda ya samu nasara.
Sannan kuma ya yi kira ga ‘yan jam’iyyar PDP a jihar su haɗa kai wajen aiki tare domin ci gaban jam’iyyar a jihar.
