Daga Alƙalamin Yakubu Lawal
Tpl. USMAN NADADA Wanda ya kasance kwararren mai tsara birane(town planner) a ilmance, ɗan siyasa ne da ke taka rawa da karbuwarsa ga jama’a kawai za ta iya yi masa gurbi a siyasance, domin ba a kira sa tsohon ɗan siyasa ba.
Saboda a shekaru har yanzu bai yi shekarun ajiye aikin gwamnati ba, duk da cewar ya fara aikinsa na gwamnati da digiri na biyu a matsayin matsakaicin ma’aikaci inda har ya kai matsayin shugaban Hukumar da ya yi aiki a cikinta,wato Hukumar tsara Birane ta Jiha.
Hon.Usman Nadada ɗan siyasa ne daga tushe da ya ɗauki lokaci ya na taka rawa a siyasa tun daga tushiya har zuwa sama, domin siyasarsa ta yi shura tun daga mazabarsa ta Wakilin Kudu II a ƙaramar Hukumar Katsina, dama jihar Katsina baki ɗaya, inda yakan taka rawar shugaban masu ruwa da tsaki ko waninsa
Wannan shuwura da Alhaji Usman Nadada ya yi ta sanya shekaru da dama a mafi yawancin tarukan siyasa ‘yan bangar siyasa da sojojin baka sukan cigaba da yi masa irin shaguɓen da ‘yan siyasa ke so , saboda yana da hannun baiwa (kyauta).
Sai dai kuma amman wannan zance bai taɓa kwadaita ma shi wani abu a zuciya ba, sai dai yakan ce “ka yi man fatan abinda ke alhairi ya fi ka ce Allah ya yi mani kaza” sannan sau da yawa yakan taka birki ga sojojin bakan da ke zuwa gidajen Rediyo don siyasantar dashi.
Saboda kasancewarsa ‘ruwa ne mai aiki sannu’. Duk da cewar a gidin maganin siyasar Katsina yake, wato inda siyasar take ɗaukar harami kuma take miƙati kafin ta fara ɗawafi
Duk da matakan da yake ɗauka na ganin mutane sun masa fatan alkhairi kawai, a maimakon haɗa addu’ar da wani muƙami.
Wannan fata ta cigaba da ruruwa musamman daga shekarar 2019, a lokacin da aka baiwa Hon.Usman Nadada kwamshiinan ma’aikatar ƙasa da sufiyo, inda har ‘yan Jarida da yake da alaƙa mai kyau da su sukan tuntuɓesa da irin wannan zance na makomar siyasarsa, inda a mafiyawan amsarsa takan zama goce-goce.
Sannan ‘yan jaridu da dama da masu fashin baki a kan makomar siyasar Katsina sukan lisafto da sunansa, musamman idan aka zo fagen neman mafita ta wanene zai gaji kujerar gwamna a Jihar Katsina, duk wannan bai sanya Hon.Usman Nadada yasa yace komai ba kai tsaye, a kan sharhi da fashin bakin da ake a kan matsayin da ake alaƙantashi da shi.
duk da cewa a gaba-gaba yake a gidan siyasar da duk waɗanda suke fitowa a siyasance tun daga dawowar dimokuraɗiyyar a 1999, aJihar Katsina sukan yi shura ne idan aka alaƙanta siyasarsu da gidan wannan hamshakin mai kuɗin a jihar Katsina (Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal).
Anan nima ina shedar cewar, Hon. Usman Nadada horon siyasar gidan Ɗahiru Mangal ne, kuma yasha nonon da bai zubar ba, don saboda buƙatarsu al’umma su amfana ga siyasa, ba su ba kai tsaye, tunda har gobe baka taɓa ganin ɗansu ko waninsu da suke nema wa gurbin siyasa ba.
Tunda ake masa irin waɗannan tambayoyi sau ɗaya na taɓa ganin Hon. Nadada ya bayarda amsa a wata jarida ta ƙasa da ƙasa ta turanci mai Suna ‘Housing Circuit Magazine’ da suka yi masa tambaya kai tsaye cewar; Idan aka tsayar da kai takarar gwamnan jihar Katsina za ka yi ko ko?.
Danƙari ga dai irin amsar da ya ba su inda ya kada baki yace.
” I _WILL ACCEPT IF NOMINATED. IF IAM NOT NOMINATED I WILL NOT GO AND HARASS MYSELF INTO LOOKING FOR THE GOVERNORSHIP. IAM NOT SCARED OF DEPEAT BECOUSE ONCE U ARE A MAN U HV TO STAND ON UR FEET; IT IS MY POLICY TO GET WHAT I CAN TO ASSIST MY PEOPLE. IT IS NOT NECESSARILY THAT U HV TO CONTEST FOR U TO ASSIST OR HELP UR PEOPLE. IAM NOT UNDER PRESSURE TO CONTEST OR SOMETHING LIKE”.Pg.25(5/May/2021).
Wannan ya nuna Hon. Usman Nadada Ruwa ne da yake tafiya a hankali, kuma da sannu cikin ikon Allah zai yi nisan da zai cika kogunan da ke kusa da nesa.
Malam Yakubu Lawal
Shi ne jami’in hulɗa da
Jama’a na ma’aikatar ƙasa
Da Sufiyo ta jihar Katsina
