Site icon Popular News

Gobe Litinin Za A Dawo Makaranta A Faɗin Jihar Katsina.

Idan Allah ya kai mu wannan Litinin ne za a dawo makaranta a zango karatu 3 a faɗin ƙananan hukumomin 34 na jihar Katsina.

Shugaban hukumar kula da ilimin bai ɗaya na jihar Katsina Lawal Buhari Daura ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Aminu Badaru Jikamshi ya fitar.

Sanarwar ta yi kira ga iyaye cewa su tura yayansu idan Allah ya kai mu Litinin 9 ga wannan watan da muke ciki makaranta.

Kuma Lawal Buhari Daura ya umarci hukumar gudanarwar hukumar, da sakatarorin ilimi, da jami’an kula da samar da ingantacce na shiyya da su saka ido akan komawa makarantar.

Exit mobile version