Site icon Popular News

Zaɓen 2023: Al’ummar Arewacin Yobe Sun Buƙaci Hon. Abba Abdullahi Nguru Ya Tsaya Takara

Daga Muhammad Maitela, Yobe

A wani taron da manya da matasa daga kananan hukumomi 6 a Arewacin Yobe suka gudanar a tsakiyar wannan makon, a garin Gashuwa shalkwatar karamar hukumar Bade, sun buƙaci Hon. Abba Alhji Abdullahi Nguru, tsohon Darakta a ma’aikatar Ayyukan Gona da raya karkara ta tarayya.

Inda suka haziƙin mutum mai kishin yankin kuma wanda ya tallafa wa ci gaban al’umma a lokacin zamansa a ƙarƙashin wannan ofis da ya riƙe, tare da bayyana cewa ta hanyar kasancewa wakili zai yi fiye da abin da ya yi a baya.

Taron ya gudana ne a ɗakin taron katafaren masaukin baki na YUSUFANA da ke Gashuwa, wanda kuma ya samu halartar ‘yan siyasa daga kowace ƙaramar hukuma- daga cikin ƙananan hukumomi shida da ke Arewacin Yobe; Bade, Jakusko, Karasuwa, Nguru, Machina da Yusufari. Wanda su ka bayyana cewa maƙasudin gangamin shi ne domin ganin haƙarsu ta cimma ruwa wajen amsa kiran al’ummar yankin.

Bugu da ƙari kuma, mahalarta taron sun jaddada cewa, “sun yanke wannan shawara ce ta la’akari da irin kwarewar da ya samu a kasancewar sa a wuraren aiki daban-daban, hakan zai bashi dama wajen ciyar da Arewacin Yobe gaba, kuma za mu bashi cikakken goyon bayan tare da tabbacin kuri’o’inmu a zaɓen 2023 mai zuwa.

Saboda haka babban burinmu shi ne ya amsa mana kira kuma ya yi maka alƙawarin tsayawa takarar da muka buƙace shi.”

“Sannan kuma Hon. Abba Alhaji Abdullahi kwararren mutum ne wanda ya san makamar aiki- ta fannin ilimi da riƙe muƙamai a ɓangarorin daban-daban, kama daga Ma’aikatar Wutar Lantarki a matsayin Mataimakin Darakta, Ma’aikatar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta ƙasa, Hukumar Yaki da Raɗaɗin Talauci ta ƙasa da makamantan su, wanda ko shakka babu zai aiwatar da kwarewar da yake da ita wajen inganta rayuwar al’ummar yankin Arewacin Yobe matuƙar muka zaɓe shi a kakar zaɓe mai zuwa ta 2023.”

A hannu guda kuma, taron ya yi tilawar wasu muhimman ayyukan raya birane da karkara waɗanda Hon. Abba ya gudanar ga al’ummar yankin, waɗanda suka haɗa da samar da hanyoyin mota, gina makarantu, tare da samar da rijiyoyin burtsatse domin samar da ruwan sha ga jama’a, tallafa wa harkokin ilimi da kiwon lafiya haɗi da samar wa sama da matasa 100 ayyukan yi a yankin da ma jihar Yobe baki ɗaya.

Har wala yau, daga cikin waɗanda suka tofa albarkacin bakinsu a wajen taron, sun kunshi matasa- maza da mata, tare da ‘yan siyasa daban-daban waɗanda suka fito daga kowane ɓangare a yankin tare da bayyana cikakken goyon bayansu, inda suka nuna cewa, “Ko shakka babu mun daɗe muna jiran wannan lokaci wanda kan al’ummar Arewacin jihar Yobe zai haɗu waje guda domin zakulo hazikin mutum, kuma karɓaɓɓe ga kowa, wanda zai iya riƙe amanar jama’a ba tare da nuna bambancin gari ko na yare ba. Lokaci ya yi wanda zamu canja yanayin yadda siyasar yankin mu ke gudana.”

“Mun daɗe muna shaukin samun gogaggen ɗan siyasar da zai tafi da kowa kuma ya kasance mai kishi. Saboda haka muna masu kira ga Hon. Abba Alhaji Abdullahi Nguru ya fito neman kujerar wakilcin Arewacin Yobe a zaɓen 2023 mai zuwa. Kuma mun yi masa alƙawarin samun cikakken goyon tare da bashi kuri’unmu.

Fatanmu kuma ya amsa kiran al’ummar wannan yanki tare da ƙoƙarin wajen riƙe amanar da muka damka mashi.” In ji mahalarta taron.

Exit mobile version