Site icon Popular News

Kabir P R O Ya Jajantawa Kungiyar Kwallon Kafa Ta Katsina United.

Ya zama wata al’adar rashin jituwa a duk lokacin da wasan kwallon kafa ya kama tsakanin kungiyoyin Nan biyu watau Katsina United da Kano Pillars. Wannan yana kasancewa Kuma ko a ina za a yi wasan.

Wannan rashin jituwa na kasancewa ne tsakanin magoya bayan kungiyoyin wasannin. Wani abun mamaki sai ka ga yadda ‘Yan Wasa da Officials ke muamulla a tsakaninsu za ka san da sauran riga a kabar magoya bayansu.

Ba zan manta ba a lokacin Katsina United (Ta Abdulmumin Aminu) idan za a yi wasa a Kano idan mun je Hedikwatar Yansanda da ke Bompai chan muke aje motocinmu, a tafi Sani Abacha Stadium a yi wasa a gama sannan a dawo a Jira sai kimanin Karfe 10 na dare Yan Sanda da Escort za su rako mu da motocinmu har zuwa Bichi sannan mu yi bankwana da su, su koma mu kamo hanyar zuwa gida Katsina.

Ya zama wajibi mahukuntan wasan kwallon kafa a Nigeria a nemo maslaha ta karshe don samun jituwa a tsakanin magoya baya sannan a dauki matakin ba sani ba sabo don gudun kara aukuwar lamarin.

Idan ba za a manta ba wannan Kungiyar wasan ita ce Katsina United hawa ta Ukku da ake samun irin wannan matsalar. Ta farko an yi ta a cikin 80th wadda su Silaka, Shegun, Jafa, Nasiru Iliya dss suka yi. Ta biyu an a Tsakiyar 90th zuwa farkon year 2000 inda aka samu Yan wasa irinsu Valdano, Arkiya, Ulterbelli, pious, dss. Sai wannan ta yanzu.

Da fatan Allah ya kara kiyaye gaba. Ameen.

Kabir Umar Saulawa
P.R.O

Exit mobile version