Site icon Popular News

Bai Kamata A Rinƙa Yi Wa ‘Yan Fim Kallon’ Yan Iska Ba. -Hafsat Hassan

Daga MUKHTAR YAKUBU.

Sabuwar jaruma a Masana’antar finafinai ta kannywwod Hafsat Hassan ta yi Kira ga masu kallon finafinai da su rinka yi musu adalci a wajen yi musu hukunci a tsakanin su da sauran Jama’a.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar da muka yi da ita a matsayin ta na jaruma in da take cewa “kada mutane su ga muna yin fim su rinka daukar mu ‘yan iska ne karuwai.

Ta ƙara da cewa sam wannan abin bai dace ba, saboda haka a daina yi masu irin wannan kalaman, domin kowanne aiki ka gani, akwai nagari akwai na banza.

Saboda haka ba a taru an zama daya ba, kowa da irin yanayin da yake gudanar da rayuwar sa. “

Daga karshe ta yi fatan yadda ta shigo harkar lafiya, Allah ya sa ta gama da harkar lafiya.

Exit mobile version