Site icon Popular News

Babu wani Masallaci Mai Suna Masjid Ummah G.R.A Katsina. -Kungiyar Izala

Daga Maman Faruk, Katsina.

Kungiyar Izala ta Ƙasa reshen jihar Katsina ta bayyana cewa bata da wani Masallaci da wani Limami ya yi ikirarin yana limanci kuma wai ya ajiye aikinsa na limanci zai tsaya takara a zaɓe mai zuwa.

Kakakin kungiyar Izala na jihar Katsina Malam Mukhtar Lawal Tsagem ya bayyana haka ga Popular News Hausa a jiya juma’a.

Idan za a iya tunawa a shekaranjiya alhamis ne, wata takarda ɗauke da sunan wani Masallaci Masjid Ummah ta taraɗe kafar sadarwa ta zamani cewa limamin Masallacin Muhammad Hasheem ya ajiye aikinsa zai tsaya takara.

Wannan takarda dai ta tada kura so sai musamman ta zo ne a daidai lokacin da al’umma suka sa ido su ga cewa masu riƙe da muƙaman siyasa sun ajiye aikinsu domin tsayawa takara, sai gashi liman ya riga su farawa.

Kamar yadda Mukhtar Lawal Tsagem ya shaidawa Wakilinmu, suma dai sun ga wancan takarda ne a kafar sadarwa ta zamani, saboda babu wanda ya kawo masu takarda cewa zai ajiye limancinsa domin tsayawa takarar a zaɓe mai zuwa.

“Kuma idan liman zai ajiye aikinsa bai kamata ya yi amfani da hatimin masallaci ba, ya kamata ya yi amfani da na shi, na ƙashin kansa, sannan kungiyar Izala bata da wani Masallaci mai wannan sunan da kuma limamin da aka bayyana cewa wai ya ajiye aikinsa” inji shi.

Popular News Hausa ta ruwaito cewa ita wannan takarda da take yawa inda har wasu ke ɗauka tamkar ta gaske ce, bata da sunan wanda aka aikawa ita, sannan babu shaidar wani ya amsa balanta a gasgata ta.

Kazalika suma ɓangaren Fityanul Islama sun tabbatar da cewa ba su da wani Masallaci na juma’a a unguwar G.R.A saboda haka ba su da buƙatar yin wata doguwar magana game da wannan batu.

Sai kuma binciken da Popular News Hausa ta gudanar ta gano cewa akwai zargin mai karfi akan wani mutum da ke tsananin adawa da takarar sakataren gwamnatin jihar Katsina da ke da hannu wajan yaɗa wannan takarda.

Batun yanzu haka yake neman zama kunfar ɗan wake, wato dai maganar tana neman riga mu gidan gaskiya, sai dai ga alama zai sake bulluwa ta wata hanyar daban.

Exit mobile version