Allah ya yi ma Alhaji Sani Dogo rasuwa da yammacin yau asabar bayan yar gajeruwar rashin lafiya.
Alhaji Sani Dogo shi ne tsohon Shugaban kungiyar kanikawa ta Jihar Katsina.
Ya rasu ya bar ‘ya ya goma sha tara a Duniya,
Daga cikin ‘yayan shi akwai Umar Sani Dogo wanda injiniya ne na gyaran motoci da Bishir Sani Dogo, wanda shima injiniya ne na gyaran motoci.
Allah ya jikanshi ya gafarta ma shi yasa aljanna fiddausi ce makomar shi, idan ajalinmu yazo Allah yasa mu cika da imani, ya amfani zuri’ar da ya bari.
