Daga Babangida Sunusi, Kano
Siyasa wata abace mai launi kala-kala kama daga wanda zai takara ko wanda zai tallata dan takara akasar nan duk da cewa dayawan siyasar kasar najeriya ba’a cika duba cancantaba amma akan zabi dantakara dan halin dayake dashi ma’ana kudi ba nasaba ba shiyasa mafi yawancin talakawa basu cika fahimtar wanene nagari ba.
Anan nakanso dayawan jama’a dasu rika duba ga irin masu halin da koda basa kan karagar mulki sukan taimaki dumbin al’umma.
Irin matashi kuma dan gwagwarmaya watau Alhaji ABUBUKAR KABIR (BABAWO) da mai girma TURAKIN ADAMAWA ya dakko matsayin daraktan magoya bayansa dan tafiyar shekara ta 2023 idan Allah yakaimu bakarim tunani yayiba dan kuwa yasa kwarya adaidai gurbinta.
Dan kuwa babu fallasa amatsayinsa na matashi kuma namatasa yasha gwagwarmaya kuma ya dade yana shanta, sannan mutum ne wanda yadade yana jaraba kasuwanci acikin birnin Kano tun daga matakin cikin anguwa har matakin kantin kwari.
Haka Kuma yarike matai daban daban amatakin shugabancin Yan kasuwa tare da kamanta gaskiya yakaishi gaccin nasara aka zabeshi matsayin daraktan magoya bayan TURAKIN ADAMAWA.
Adan abinda nasani ga ALH ABUBUKAR KABIR BABAWO matsayinshi na matashi kuma mai zuciyar neman nakanshi yasamu damarmaki inda Kuma yayi amfani da wannan dama ta taimakon matasa wajen kasuwanci tare da bangaren gwamnati wanda haryazuwa yanzu bai gyaza bai kumayi kasa agwuiwaba.
Koda yake bansani ba ko ATIKU ABUBUKAR yasan Mai girma DG support nashine tun lokaci Mai tsayi, idan kau baisanshi ba to ashawarata yakara rikeshi dan kuwa insha Allahu zai kai ga cin nasara dan yadakko wanda yadace batare da kwadayi ba ko kallon mai zai samu sai dai yaza’ai wajen ceto al’ummar najeriya daga halin damuke ciki yanzu.
Sannin kowane ga wadanda suke bibiyar siyasar Mai girma TURAKIN ADAMAWA yadade yana bukatar kawo chanji da dauki ga Yan najeriya bayan rawar daya taka lokacin dayake mataimakin shugaban kasa watau lokacin dayake tare da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo inda suka taka rawargani da zan iya cewa har yakawo yanzu ba’a kara irin ayukan dasukayi ma wannan kasaba.
Kuma ni ara’ayina Kuma aganina marama TURAKIN ADAMAWA baya yazuwa cimma nasara azabe mai zuwa dan kuwa baya tunanin tara kudi dan kuwa yanadasu batare da tunanin yadda zai fara tarawa wasu kudi.
Hakazalika kowa yasan babu abin yake Kara kawo cigaba ga kasa Wanda yawuce kasuwanci Kuma kowace kasa bata tunbatsa sai ta hada da kasuwanci,kuma shi Atiku Abubakar dan kasuwane Kuma yadauki jama’a dayawa awannan bangare nakasuwanci inda shi kansa bai San adadin al’ummar dake cin abinci akasanba ahalin yanzu.
Kuma yadda Atiku ya dakko matashi na matasa to lallai ya dauki hanya dodar wajen samun nasara madamar Babawo ne zai cigaba da jagoranci wannan tafiya ta magoya bayansa akasar nan.
Nima anan zanyi amfani da wannan damar nacewa kada mubari wannan damar ta kubce mana wajen marama TURAKIN ADAMAWA baya dan kuwa akwai tunani mai kyau tare da mafita wajen tsamo kasar nan daga nutso da wasu Yan bani na iya suke tafiya da ita batare da hawan hanyar data daceba.
