Daga Abdulrazak Bello Kaura
Maganganun masana Harkar Tsaro da Kuma Diflomasiyya.
Kasashen Biyu Duba Dan-Juma ne da Dan-Jimmai. Da harshe guda suke magana (Yare) kuma ko wanen su Nada muradin da yake son ya cimma.
ABUN LURA
Kasashen nan suna Kera miyagun Makamai, kuma idan gomnatochi ba su saye ba sai su sayar ma ‘yan kasuwa (Black Market) su kuma sai su sayarma duk mai so, sai a shigo da su kasahen musamman na Afrika daga ciki hadda Nigeria.
Wani Masani ya tabbatar man cewa, idan suna Fada da junan su, babu zancen a sayar da makaman balantana a kawo su wurin da ake kashin bayin Allah domin suma suna bukata don kare Kasashen su.
Kenan fadan a tsakanin su Alkhairi a wurin Yan Nigeria amma a fakaice.
Shi Kuma retired Major Muhammad Bashir Shu’aibu mni Wanda tsohon jami’in leken asiri ne a rundunar Sojin Nigeria Wanda yayi aiki a Koriya ta Kudu da Kuma Misrah yace Sam bai dace Shuwagabannin Nigeria su goyi bayan wani bangare ba a cikin Kasashen Biyu. Sai dai su bada shawara ayi sasanci.
Yace, Rasha ta taimaki Nigeria da makamai da sauran kayan yaki a lokacin Yakin Basasa, yace kuma ko yanzu (ba a fada) idan wani rikici ya barke a Nigeria za a nemi agajin Rasha, don ko yanzu makaman su sune suka fi yawa a kasar nan (kamar irin AK47 da Harsashi na musamman mai kabrin 7.62mm da irin bindigar nan Duksha)
Yace Rikicin ya samo asali ne tun a Shekara ta 1961 a tsakanin Kasashen na Rasha da Ukiren da irin su Belarus (da suka fi karfi ga Rasha) da yankin Kiremiya da dai sauran Kasashen NATO.
Saboda haka zai fi kyau mu kama Bakin mu muyi addu’a Allah ya tsare mu ya kuma tabbatar mana da alkhairi.
Wani rikici alkhairi ne wani kuma matsala ce.
Abdulrazak Bello Kaura
Development Journalist
