Daga shafin Saifullahi Mato Kankara
Alhamdulillahi, an sako ‘yan uwanmu su 42 da akai garkuwa dasu. Matan Aure 19, ‘yan mata 7 duk da Amarya, sai kananun yara. Suna cigaba da jinya da amsar magani.
Muna godiya ga Allah, da kuma godiya gareku bisa addu’o’in da kukai tayi ba kakkautawa.
Allah ya saka maku da Alkhairi, ya kara bamu zama lafiya da kwanciyar hankali a kasarnan.
Idan za a iya tunawa kimanin mako biyu da ya wuce mun baku labarin sace wadanda mata kamar yadda Saifullahi Mato ya ambata.
Sai dai har zuwa yanzu da aka samu nasarar dawowarsa gida jami’an tsaro a jihar Katsina ba su komi ba game da kuma sako su.
Muna fatan Allah ya kara kiyaye gaba. Amin summa amin
