Gwamnatin tarayya ta bayyana damuwarta game da sabon matakin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ta ASUU ta shiga da cewa ba su abinda ya da ce ba
Yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta shiga a matsayin wanda bai dace ba domin babu wata sanarwar yajin aikin da aka samu daga shugabannin kungiyar ta baki da baki ko kuma a rubuce.
Sai dai kungiyar daliban Nijeriya ta kasa ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta korar ministan ilimi Malam Adamu Adamu da ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Dr Chris Ngige saboda gazawa wajen warware takaddamar da ke tsakanin kungiyar malaman jami’o’i da gwamnatin tarayya.
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, yayin da yake mayar da martani game yajin aikin ya ce kungiyar ta ASUU ba ta sanar da shi cewa suna yajin aikin ba.
Adamu ya yi magana ta bakin Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar Mista Ben. Bem Goong.
DCL Hausa
