Daga shafin Maiwada Dammallam
Da farko dai, matsalar doka che, da alkalai, wani lokachi da yansanda da gwamnoni.
- Ya kamata, majalisun mu su yi wasu special courts wadanda ke da alhakin sauraron shariar kidnapping kawai.
- A sama kotunan nan time frame na wata ukku dole ne a gama shariar chikin wata ukku.
- Babu beli a chikin maganar kidnapping. Har sai an gama sharia.
- Hukunchin kisa bisa rataye wa a baynar jamaa, ko kuma a prison amma a nuna wa mutane a television din su.
- Bayan yanke hukunchi, ba sai an jira gwanma ya saka ma dokar hannu ba. Ya kamata dokar ta tanadi chewar muddin gwanma ba yaki yadda da hukunchin ne ba a rubuche, to dole ne a rataye Wanda a ka yanke ma hukumchin bayan chika wata daya da zartar da hukunchi.
Maganar gaskiya ita che, hukomomi suna na su kokarin, amma saboda mutane ba sa ganin makomar wadanda a ke kamawa da zargin kidnapping ga ni su ke duk sakin su a ke yi bayan an daidaita da alkalai.
Hakan na faruwa, amma mafi yawanchin su an kashe su, to amma tun da babu hujjar hakan, mutane gani suke su na nan daram da lafiyar su.
Dole ne a nuna wa mutane a zahiranche, faranshin da mutum zai biya Idan ya shiga kidnapping.
Farashin kuwa shine kisa a bayyane ta hanyar rataye wa, kuma a chikin wata 4 kachal.
Aminu Abubakar Danmusa
