Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Rundunar’Yan Sandan jihar Katsina ta tabbatar da kama wani mai suna Abubakar Abdulbasir dan shekara 18 da ke zaune a garin Marabar Kankara da ke karamar hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya bayyana haka a lokacin da yake baje kolin wadanda ake zargi da aikata laifufuka daban-daban a shalkwatar Yan sanda da ke Katsina.
Gombo Isah ya kara da cewa wani mutun mai suna Sunusi Abubakar ne ya kai rahoto a caji ofis din ‘yan sanda cewa diyarsa yar shekaru 4 mai suna Halimatu Abubakar ta yi batan dabo.
A cewarsa sai mutumin ya ce daga baya aka kirashi da waya ana gaya masa cewa an yi garkuwa da diyarsa ana neman kudi naira dubu 70,000 ko Kuma ta rasa rayuwarta.
” Da jin wannan labarin sai jami’an’yan sanda na bangaran yaki da masu garkuwa da mutane suka fara aikinsu wanda daga karshe suka yi nasarar damke wanda ake zargi da aikata wannan baban aikabai’i Abubakar Abdulbasir.” Inji shi
Kakakin rundunar SP Gambo Isah ya ce a lokacin da jami’an tsaro suke gudanar da binciken wanda ake zargi ya amsa laifinsa, inda ya ce shi ya dauke ta ya ajiyeta acikin wani kangon gida a garin Marabar Kankara da ke cikin karamar hukumar Malumfashi.
Tuni dai aka kubutar da wanann karamar yarinya aka hada ta da iyayenta, ba tare da ta samu wani rauni ba ko cutarwa.
Daga karshe SP Gambo Isah ya bayyana cewa da zaran sun kammala bincike za su tura keyar wanda ake zargi zuwa gaban kuliya bantam sabo domin daukar matakin shari’a akan sa.
