Mataimakin Gwamnan jihar katsina QS Mannir Yakubu ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC ta karamar hukumar katsina a karo na uku.
Makasudin taron dai shine cigaban tattaunawa kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi fitar da yan takarar da zasu shiga zabubbukan kananun hukumomi da kansilolin su na karamar hukumar katsina.
A taron shugaban taron mataimakin Gwamna ya bayyana bayanan kudi na abinda ke akwai a cikin asusun zauren na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar ta karamar hukumar katsina. Kudin da yayan jam’iyyar suka hada da kan su, tun lokacin da za’a aiwatar da aikin sabunta rijistar jam’iyyar.
Wanda ya bayyana sauran kudaden da sukayi ragowa agaban kowa da kowa, Tare da kaddamar da cigaba da amfani da su a wurin tafiyar da harkokin zauren wadanda kudi ke bukata.
Mahalarta taron sun hada da shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar katsina da sakataren jam’iyyar na karamar hukumar katsina, da Danmajakissar dokoki na karamar hukumar katsina Hon. Ali Abu Albaba, da Kwamishinan wasanni da bunkasa jindadi da walwalar al’umma na jihar katsina, Babban sakataren hukumar tsaftace muhalli Alh Isah Barda.
Sun hada da babban daraktan sababbin kafafen sadarwa na Gwamnatin jihar katsina Alh Al-ameen Isah kofar kaura, da Darakta a hukumar muhalli ta jihar katsina Alh Abubakar Muhammad Gege Babban Sakataren Hukumar Jin kai da Agajin gaggawa Alh Babangida Nasamu da SSA Alh Sabo Musa, da SA Alh Abdul Aziz Mamuda da Alh Aminu Ashiru kofar sauri, Alh Dahiru Gambarawa da Alh Kabir liman, SSA Alh Tanimu Sada Sa’ad da Amb. Yakubu sule da Alh Mustapha wada protocol da Alh Babangida wayya sauki fish, da Alh Bala saulawa Danmasanin magajin garin katsina.
Sauran sun hada Alh Yusuf Barmo masanawa da babban sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar katsina Dr. Kabir Mustapha da babban sakataren ofishin mataimakin Gwamna Alh Aminu Abu Bazariye, da babban mai taimakama mataimakin Gwamna akan dukkan muhimman ayyuka Alh Yahaya Aliyu da dai sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar katsina duk sun halarci wannan taro sai wadanda suka bada uzuri.
Muhammad Barmo SA To His Excellency Deputy Governor Of Katsina State On New Media.
