Site icon Popular News

Zamu Shiga Zaban Kananan Hukumomi Babu Gudu Babu Ja Da Baya –Majigiri

Daga Maman Faruk, Katsina

Bayan zama da Shugaban Jam’iyar PDP na jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas,) Ya bayyana cewa Jam’iyar PDP zata shiga zaben Kananan Hukumomi babu gudu ba ja da baya.

Hon. Magijiri wanda yabbaya cewa Jam’iyar PDP zata ba Matasa dama su taka rawa a kowane bangare domin duk inda babu Dan koyo to gwani karewa yake musamman a sha’anin siyasa da take bukatar matasa a wannan lokaci.

Sanan ya kara jaddada cewa PDP ta ba kowane dan Jam’iya dama ya fito yayi takara ba dole sai wani ba, ko dan wani, ko yaran wani, ko waye Kai zaka iya tsayawa takara kofa a ude take.

“Domin PDP tana da manufar ba kowane matashi dama lura da zabar Matashi a matsayin shugaban matasa a matakin national level zai karawa jam’iyyafr kwarjini da kuma kima azaban 2023.” Inji shi

Shugaban jam’iyyar ya ce yanzu hak kofa a bude take ga dukkan matashin da ya ga zai iya bada wata gudunmuwa tun daga matakin Ward har local Government, muna ta cewa an ki gyarawa to mu me zai hana mu fito mu gyara?

Dukkan matashin da ke da ra’ayin ya yi takara domin kawo sauyi ga jama’ar yankinshi a inuwar Jam’iyar PDP to ya tuntubi daya daga cikin ‘yan wannan kungiya ta Matasan PDP na jihar Katsina

Exit mobile version