Site icon Popular News

Bikin Karin Shekara: An Bayyana Tarihin Lamis Dikko A Matsayin Daya Daga Cikin Nagartattun Mutane Masu Dattako Da Fada Aji A Najeriya

Daga Ambasada Nuradeen Adam Kankara Tina

Alh. Lamis Dikko sanin kowane a jihar Katsina da kuma kasa baki daya, mutum ne wanda yake da dattako da fada aji tare da girmama al’umma.

Lamis mutum wanda ya shafe shekaru da dama yana gwagwarmayar siyasa domin kawo ma al’umma cigaba mai mana’na wanda kuma har yanzu cigaba da wannan fafutika.

Alhaji Lamis Dikko ya samu digirinsa na farko daga babbar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya kammala  digirinsa na farko akan tattalin arziki, haka zalika yayi digirinsa na biyu a jami’ar kasuwanci ta harvard da ke London inda ya samu digiri na ukku  a fannin ilimin kimiya.

Alhaji Dikko ya fara aikinsa ne a gidan rediyon jihar Kaduna a matsayin mai gabatar da labarai da al’amuran yau da kullum, daga bisani kuma ya tashi zuwa jaridar standard ta Najeriya a matsayin babban edita.

yayi karatutuka da dama a kwalejin nazarin harshe a Zariya kafin ya fara aiki a babban bankin Habeb a Nijeriya. haka kuma yayi aiki a bankin Intercity a shekarar 1998 a matsayin janar manaja kuma ya rike manajin Dirakta daga 2001 zuwa 2005.

Ya kuma ya yi darakta mai gudanarwa a Kamfanin tabbatar da amfanin mutuntuwa da kuma yayi aiki a hukumar babban bankin kasuwanci .

Baya ga haka kuma Alhaji Lamis Shehu Dikko ya kasance babban darakta a babban bankin kasuwanci (Unity Bank).

Daga bisani yayi takarar kujerar Sanatan Katsina ta tsakiya a shekarar 2015 kuma har yau har gobe yana cikin masu fada aji na PDP na jihar Katsina da Najeriya baki daya.

Bai tsaya nan ba, har yau har gobe shine ajiyan Katsina, kuma daya daga cikin wanda masarautar Katsina ke daratawa da girmamawa wannan shine takaitatcen tarihin sa, kusance tare da mu “domin jin daga bakin mai ita”

Exit mobile version